A ranar Litinin ne Majalisar Dattawa ta tantance Dakta Mariya Mairiga Mahmud bunkure wacce ta Maye Gurbin Maryam Shetty a matsayin minista daga jihar Kano.
Majalisar Tsara Tattalin Arziki ta Kasa (NEC) ta umurci Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) da ta gaggauta raba hatsi ga jihohi nan da mako guda ko biyu domin karya farashin kayayyakin abinci a fadin kasar nan, gwamna Bala muhammad na Bauchi ne ya bayyana hakan bayan futowar su daga taron tattalin arzuki na kasa.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu a ranar Laraba da daddare ya yi muhimmiyar ganawa da wasu manyan jiga-jigai dangane da halin da tattalin arziƙin ƙasar nan yake ciki.
Alamu masu ƙarfi da suka fito da yammacin ranar Laraba, 19 ga watan Yuli, sun nuna wanda shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ke son ya zama sabon shugaban jam'iyyar APC.
Shugaban NNPCL, Mele Kyari, ya bayyana cewa babu ruwan Gwamnatin Tarayya da ƙarin kuɗin fetur,kasuwa ce tayi karin sakamakon yanayi a nan gaba farashin ka iya faduwa warwars.
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ne ya bayyana wa ma’aikatan Nijeriya tabbacin shirin gwamnati na sake duba yiwuwar karin albashi ga ma’aikata don rage radadin cire tallafin man fetur
Shugaban kungiyar nema wa nakasassu masu bukata ta musamman mafita da ke Kano, Abdulrazak Ado Zango ya ce dakagtar da albashin sabbin ma’aikata sama da dubu 10 da gwamnatin Injiniya Abba Kabir ta yi abun ya shafi nakasassu sama da 150 wanda ya sa suka shiga tsaka mai wuya.